Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Kwamitin Tsaro Domin Zabe A Jihar Kano


Sojoji suke sintiri da motar sulke.

Kwamitin ya hada dukkan wakilan hukumomin tsaro.

Cibiyar ta musamman zata kunshi wakilai daga rundunar 'Yansanda da ta Soja, da wakilan hukumar tsaron 'Yansandan farin kaya watau SSS, da hukumar kastam, da hukumar shige da fice watau Imagirashon.

Saura sun hada da hukumar Civil Defense, da kuma hukumar kiyaye hadura ta kasa.

Wannan cibiya zata kasance karkashin jagorancin kwamishinan 'yansanda na jihar Ibrahim Idris. A bayanan da suka fitar, sun ce aikin kwamitin sun hada harda sanya ido kan yadda al'amura zasu rika wakana a sassa daban daban na na jihar kano a lokutan zabe da kuma bayan an kammala zabe.

Wannan cibiya zata rika karbar bayanai ko korafe korafe daga jama'a ta woyar tarho domin daukar mataki.

Haka kuma cibiyar ta fitar da ka'idoji da jama'a zasu kiyaye daga ranar jumma'a 27 ga watan nan.

Ga karin bayani.

ZABEN2015: An Kafa Kwamitin Tsaro Domin Zabe A Jihar Kano - 3'23"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG