Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Moon Jae-in Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Koriya ta Kudu


Moon Jae-in wanda ya lashe zaben shugaban kasar Koriya ta Kudu
Moon Jae-in wanda ya lashe zaben shugaban kasar Koriya ta Kudu

Sakamakon da aka soma samu daga zaben shugaban kasar da ake a Koriya ta Kudu (KTK) na nuna cewa dan takaran jam’iyyar D-P-K, Moon-Jae ne ke nuna alamar lashe zaben.

Binciken da kafofin watsa labarai na KBS, MBC da SBS suka gudanar duk sun nuna cewa Moon ya kwashe 41% na kuri’un da aka jefa.

Wannan kiddidigar dayi daidai da hasashen da aka yi tun kafin zaben, wacce ita ma ta nuna cewa Moon ya bada tazarar akalla kashi 20% akan sauran ‘yan takara 13 dake cikin zaben.

Rahottani sunce mutanen da suka fito jefa kuri’a suna da dimbin yawan gaske a sanadin cece-kuccen da aka fuskanta dangane da dambarwar abin assha na milyoyin daloli da tsohuwar shugabar KTK din, Park Geun-hye ta sami kanta ciki, abinda ya janyo tarukkan zanga-zanga na makkoni kuma har ya kai ga sa Majalisar Dokokin kasar ta tsige ta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG