Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mubarak Ya Ki Amsa Laifi A Farkon Shari'a Mai Tarihi


Jami'an tsaro kenan ke fama da jama'a a lokacin shari'ar Mubaraka

Kasar Misra ta fara shari’ar tsohon shugaba Hosni Mubarak, wanda ya

Kasar Misra ta fara shari’ar tsohon shugaba Hosni Mubarak, wanda ya halarci kotun bayan kusan watanni 6 da hambarar da shi a wani juyin juya hali na kwanaki 18 na bukatar sauye-sauyen dimokaradiyya.

Mr. Mubarak ya yi watsi da dukkannin tuhumce-tuhumcen da ake masa a zaman kotun a birnin al-Kahira. A tsawon zaman kotun ya kishingide ne kan wani gadon Asibiti da ke cikin wani katon kejin da aka gina a gaban kotun inda dukkanin wadanda ake zargin za su shi.

Ana zargin tsohon shugaban na Misra da laifin bayar da umurnin kashe masu zanga-zangar kyamar gwamnati a yayin juyin-juya halin da ya kai ga hambarar da shi. Kusan mutane 900 ne aka hallaka a yayin wannan tashin hankalin.

Mr. na fuskantar hukuncin kisa idan an same shi da laifi. Ana kuma zarginsa da rashawa da cin hanci, da amfani da iko ba bisa ka’ida bad a kuma sama da fadi da dukiyar al’umma.

Su ma ‘yayansa biyu, Alaa da Gamal, sun fuskanci shari’a a yau Laraba, inda su ka tsaya kafada da kafada da Mr. Mubarak sun a kuma magana das hi a lokacin zaman kotun. Su ma sun karyata zarge-zargen da ake masu.

Sauran wadanda aka fara shari’ar ta su sun hada da tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida a karkashin gwamnatin Mubarak wato Habib al-Adly, da manyan jami’an ‘yan sanda, da kuma wani hamshakin dan kasuwa mai suna Hussein Salem.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG