Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muguwar Guguwar Maria Na Cigaba da Haddasa Barna a Yankin Carribean


Irin barnar da mahaukaciyar guguwar Maria ta haddasa a Puerto Rico
Irin barnar da mahaukaciyar guguwar Maria ta haddasa a Puerto Rico

Bayan da tayi raga-raga da tsirin Puerto Rico mallakar kasar Amurka har yanzu muguwar guguwar mai suna Maria na cigaba da haddasa barna a yankin Carribean.

Guguwar Maria ta ci gaba da kadawa yau jumma’a da safe da karfin gudun kilomita dari biyu da biyar a awa guda.

Kudu maso gabashin Buhamas ma zai fuskanci guguwar da ta tafka ruwa a Puerto Rico da jamhuriyar Demonican.

Yanzu haka dai guguwar dake da karfin maki uku ta kada Peurto Rico ne da karfin maki hudu ranar Laraba ta sanya ambaliyar ruwa a wurare da dama , ko da yake bata yi barna ainun ba, duk da haka ta shafi wurare da dama a Damonican Republic

Wannan ce guguwa mafi karfi da aka fuskanta a yankin na Peurto Rico dake karkashin Amurka cikin kusan shekaru casa’in. gwamnan yankin Ricardo Rossello yace, akwai bukatar agajin gaggawa a yankin.

Kawo yanzu ba a iya tantance barnar da guguwar tayi ba, kasance har yanzu ba a iya shiga yankin. Sai dai akwai rahotannin dake nuni da cewa, ana fama da ambaliyar ruwa da tabo.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG