Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhawarar Kwararru Kan Karya Darajar Naira A Najeriya


Kudaden Najeriya.

Kwararru kan tattalin arziki a Najeriya, na ci gaba da tafka muhawara kan alfanu ko rashin alfanun rage darajar Naira a kasar.

A yan kwanakin nan dai sai da farashin dalar Amurka ta kai har Naira 400 a kasuwar bayan fage, yayin da a hukumance take Naira 199. Alhaji Mohammadu Mustapha Muntube, tsohon babban manajan daraktan Bankin Jaiz wanda yake masanin tattalin arziki. Na ganin kafin ayi gyara dole ne a matsar da darajar Naira ta kai kamar 250 a hukumance, haka kuma dole ne babban banki ya dauki matakan da suka kamata.

Shi kuma wani kwararre kan tattalin arziki a Najeriya, Abubakar Ali, na da ra’ayin da ya banbanta da na Alhaji Mohammdu, inda yace idan har aka mayar da Dala ta koma Naira 250 a hukumance to tabbas kasuwar bayan fage zata koma 500, a cewarsa haka al’adar kasar take.

A karin hasken da Muhammadu Mustapha Bintube yayi, yace yakamata babban bankin tarayya ya san yadda zai yi ya dauki matakan da sauran kasashen duniya ke dauka na yadda kudadensu basa canzawa a kasuwa.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG