Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhawarar Yan Takarar Mataimakan Shugaban Kasar Amurka


Muhawarar 'yan takarar mataimakan shugaban kasar Amurka

Jiya da dare, ‘yan takaran mataimakan shugaban kasa a zaben shekarar nan na Amurka, Tim Kaine (Democrats) da Mike Pence (Republicans) sun gwa bza a muhawarar da suka yi, inda suka tabo batutuwa da dama, kuma suka yi kokarin matsayin iyayen gidajen su akan batutuwa da dama da suka hada da maganar bakin haure, tattalin arziki, da tsaro.

Milyoyin mutane sun kalli mutanen biyu, musamman da yake an san cewa kowannensu na iya darewa kan kujerar shugabancin kasa idan wani abu ya sami wanda suke rufawa baya.

‘Yan siyasan biyu, wadanda dukkansu sun yi gwamna kuma sun yi zaman ‘yanmajalisar dattawan Amurka (Sanatoci), watakila kan abu daya kawai ra’ayinsu yazo daya – bukatar samar da fahimtar juna tsakanin ‘yansanda da al’umma.

A cikin muhawarar, Tim Kaine, wanda tsohon gwamnan jihar Virginia ne,ya zargi Donald Trump da cewa baya ganin kowa da gashi, kowa cin mutuncinsa yake:

Tim Kaine yace a lokacin da yake yawon kyamfe, Donald Trump ya kira ‘yan kasar Mexico a matsayin masu yin fyade kuma masu aikata laifukka. Haka kuma ya kira mata sakarkaru, aladu, karnukka, munana, ya kuma ce bakaken fata suna zaune a cikin bakar ukuba, kai karshenta ma yace shugaban Amurka na yanzu, Barack Obama, ba haifaffen Ba’amurke bane, dan asali.

Daga nan ne shi kuma Mike Pence, wanda shine gwamnan jihar Indiana, yace ai abubuwan da Donald Tgrump ke fada kamar wasar yara ne idan aka kwatanta da abinda Hillary Clinton ke fada:

Mike Pence yace koda Donald Trump ya fadi duk abubuwan da kake zargin ya fada kuma a fasalin yadda kace ya fade su, ba zasu kai ko kamun kafar abubuwan da Hillary Clinton ke fada ba, kamar lokacinda da ta hada hancin magoya bayansu, ta kira su da sunan “lalattattu, abin kyama.”

Haka kuma maganar harajin da aka ce Donald Trump baya biya, ta kunno kai, inda dan takaran mataimakin shugaban kasa na Democrats ke cewa:

Tim Kaine yace sai da Gwamna Pence ya nunawa Donald Trump takardunsa na biyan harajin don nuna cewa ya cancanci ya zama mataimakin shugaban kasa, saboda haka dole Donald Trump ya nuna wa Amurkawa takardunsa na haraji – inda Mike Pence ya maida murtani da cewa... “ ai Donald Trump ya gabatarda fiyeda shanfuna dari na bayanan harakokinsa da suka shafi kudade, wanda shi kadai ne abinda doka ta bukace shi da yi.

A ranar Lahadin nan mai zuwa ne dai za’a gwabzawa karo na biyu tsakanin Donald Trump da Hillary Clinton a birnin St. Louis.

XS
SM
MD
LG