Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimmancin Cancanta Wajen Raba Mukamai


Shugaban Najeriya mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari a tsakiya tare da wasu gwamnonin kasar.

Yayin da gwamnati mai jiran gado ke shirin karbar mulki a wasu ‘yan makwanni masu zuwa, yanzu haka hankula sun karkata ne kan wadanda za a baiwa mukamai, inda masana a harkar gudanar da aiki ke kira da a duba cancanta.

A kasashe masu tasowa musamman ma a nahiyar Afrika, akan raba mukamai ne bisa la’akkari da wanda mutum ya sani ko kuma bisa yanki, kamar yadda ake gani a Najeriya, amma hakan masana sun ce ka iya haifar da cikas ga aikin da ake so a yi har da ma shi kansa wanda aka baiwa mukamin.

Comrade Shehu Muhammad na kungiyar kwadago a Najeriya na daya daga cikin masana da ke ganin yin hakan zai iya shafar aikin da za a yi.

“Idan aka ce an kawo wanda bai cancanta ba yana shafar ainihin aikin da zai yi da gudunmuwar da zai ba da.” Comrade Muhammed ya ce.

Ya kara da cewa yana da muhimmaci a samu mutanen da su ke tare da mutanensu sannan su kasance suna da kishin ba da gudunmuwarsu wajen ci gaba kasa baya ga haka su san aikin da za a basu su yi.

A lokuta da dama akan raba mukamai ma har ta hanyar wadanda suka yiwa jam’iyya aiki ko kuma hidima, amma Comrade Muhammed y ace al’uma za ta fi ci gaba idan aka baiwa cancanta fifiko.

“A halin da muke ciki a Najeriya mun fi bukatar cancanta bisa ramuko na kyamfen da aka yi.” In ji Comrade Muhammed.

A baya akwai rahotanni da ke cewa wasu gwmanoni sun kaiwa shugaba mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari, sunayen mutanen da suke so a baiwa mukamai in an tashi rabo, amma ya ki amincewa da wannan bukata ta su, kuma a cewar comrade hakan ya yi dai dai.

“Mu mun yi farin ciki da haka domin a yanzu ne muka san cewa an sa turban a shugabancin da za a samu ci gaba.” Ya kara da cewa.

Ga karin bayani a hirar Usman Kabara da Comrade Shehu Muhammed:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG