Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimmancin Musayar Bayanan Sirri Tsakanin Kasa Da Kasa


Shugaba Mohammadu Buhari
Shugaba Mohammadu Buhari

Shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari ya ‘kara nuna muhimmancin ‘kara samar da bayanan sirri masu inganci tsakanin kasa da kasa.

Domin duniya baki daya ta hada kanta wajen yaki da ta’addanci wanda ke ci gaba da yin barazana ga al’ummar duniya. Shugaba Buhari dai yayi wannan bayaninne alokacin da yake karbar takardun jakadun kasashen Tunisia da Jamus da Sweden da kuma Canada.

Inda yake cewa samar da bayanan sirri ingantattu babu shakka zai kara da baiwa kasa da kasa karfi wajen yaki da ta’addanci bai daya. Ganin cewa ana durkusar da kasashe masu tasowa kuma ana kara kashe mutane masu yawan gaske a cikinsu, balle kuma kasashe masu tasowa kamar Najeriya.

Da yake ganawa da jakadan kasar Canada Mr. Christopher Thornley, Shugaba Buhari yace akwai bukatar nan take a bayar da bayanan sirri ba tare da jinkiri ba, saboda zai taimaka kwarai da gaske wajen karya lagon ta’addanci da duniya ke fuskanta musamman ma Najeriya.

Saurari rahotan Umar Faruk Musa daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

XS
SM
MD
LG