Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mukaddashin Gwamnan Taraba Ya Gana da Sarakunan Jihar Akan Tsaro


Alhaji Abubakar Sani Danladi, mukaddashin gwamnan jihar Taraba

Wannan shekarar ta ga salwantar rayuka da dama a jihar Taraba sabili da rigingimun kabilanci da na addini.

Sabili da samo bakin zaren matsalar tsaro a jihar Taraba yanzu sabon mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Danladi ya gana da sarakunan jihar.

A ganawar da yayi da sarakunan mukaddashin gwamnan yayi barazanar daukan mataki akan duk wadanda suke da hannu akan rikice-rikicen da suka addabi jihar. Yace ya gayawa sarakunan cewa idan suka dogara kawai akan 'yansanda da sojoji ba zasu samu biyan bukata ba. Su sauwakawa kansu su kuma sauwakawa gwamnati su fada ma juna gaskiya.

Ta wurin fadin gaskiya za'a samu zaman lafiya. Rashin gaskiya ba zai kawo zaman lafiya ba.Sarakuna su fitar da duk mutanen da suka tabbatar miyagu ne su mikawa jami'an tsaro. Idan sarakuna sun yi shiru basu taimaki jami'an tsaro ba babu inda za'a je da tsaro. Dalili ke nan mukaddashin gwamnan ya nemi sarakuna domin ya ji ra'ayoyinsu da shawarwarinsu.

Sarkin Mumuye Alhaji Ado Adamu yace lokaci yayi da al'ummomin Taraba zasu koyi zaman tare. Su yi hakuri da juna su zauna lafiya. Su yi hakuri, rai na Ubangiji ne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

XS
SM
MD
LG