Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mulkin Karba-Karba Ne Kawai Mafita Ga Najeriya - Gowon


Tsohon Shugaban Najeriya Gen. Yakubu Gowon
Tsohon Shugaban Najeriya Gen. Yakubu Gowon

Tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya Yakubu Gowon, ya yi kiran da a bi tsarin shugabancin kasar na karba-karba a tsakanin manyan yankuna 6 na kasar.

A jawabin da ya yi a wajen taron bikin cika shekara 100 da kafuwar kungiyar tsofaffin daliban kwalejin Barewa ta Zariya da aka gudanar a Abuja, Gowon ya ce tsarin karba-karba na shugabancin kasar, babban gimshiki ne na samar da zaman lafiya, adalci da raba dai-dai, da kuma ci gaban kasa.

Haka kuma ya bayyana bukatar zagayawa da mukamin na shugabancin kasar ga dukkan jihohi 19 na Arewacin kasar idan nasu lokacin ya zo, yana mai cewa ba wata kabila da ta fi wata.

Tsohon shugaban na mulkin soji ya ba da shawarar a rika yin mataimakan shugaban kasa biyu, inda daya zai fito daga yankin da shugaban kasa zai fito, yayin da na biyun kuma za’a zabe shi a kashin kansa a lokacin gudanar da zabe.

Yankuna 6 na Najeriya
Yankuna 6 na Najeriya

Bugu da kari a matakin jihohi ma, Gowon ya ce kamata ya yi a rika tsarin karba-karba na kujerar gwamna a tsakanin yankunan ‘yan majalisar dattawa 3 da kowace jiha take da su.

Ya ce yin haka zai magance korafe-korafen da wasu al’ummomi ko kabilu suke yi na cewa ana mayar da su saniyar ware.

Da ya juya akan sha’anin tsaro, Yakubu Gowon ya ce sunan da yankin yankin Arewa ya yi a haujin zaman lafiya ya wargaje, sakamakon yawaitar ayukan ta’addanci a yankin.

Ya ce “rashin tsaro yana barazana ga samun ci gaban kowace kasa,” don haka ya ce ya zama wajibi a dauki tsauraran matakan tabbatar tsaro, domin samar da damar zaman lafiya da ci gaba a Najeriya.

Haka kuma yayi kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki, da ma dukkan ‘yan Arewa, da su ba da gudummuwa wajen dawo da kima da martabar yankin na zaman lafiya da kwanciyar hankali.

XS
SM
MD
LG