Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunan Yanayi Ya Halaka Mutane 18 A Kudancin Amurka


Hadarin motoci da mugun yanayi ya haddasa a wani yankin Amurka

Hukumar kula da yanayi ta kasa ta fada jiya Lahadi cewa sassan kudancin jahar Georgia, da arewacin jahar Florida, kuma yankin kudu maso gabashin Alabama zasu iya fuskantar mahaukaciyar guguwa da kuma ruwan sama masu karfin gaske.

Mutane 14 ne mahaukaciyar guguwar da ruwan sama suka kashe a jhaar Georgia a karshen mako. Wasu mutane hudu kuma guguwa ta kashesu a jahar Mississipppi ranar Asabar.

Gwanan jahar Georgia Nathan Deal ya ayyana dokar ta baci a sassan da bala'in ya afkawa. Tuni shugaban Amurka Donald Trump ya zanta da Gwamnan inda ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda bala'in ya shafa.

Haka nan shugaban na Amurka ya bayyana aniyarsa na yin magana da gwamnan jahar Florida Rick Scott.

XS
SM
MD
LG