Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunar Ambaliyar Ruwa Ta Afkawa Jihar Louisiana


Masu aikin ceto

Gwammnan jihar Louisiana dake Amurka, wadda mummunar ambaliya ta afka mata ta gargadin jama'ar jihar jiya Lahadi, da suyi hattara yayin da ruwan ambaliyar kekara yawa. Haka kuma masu aikin ceto na ta kokarin ganin sun tsamo dubban mutanen da wannan ambaliyar ta rutsa dasu.

Gwamnan jihar John Bel Edward, yace mutane dubu 7 ne a jihar daga Kudu maso Gabashin jihar aka ceto daga gidajen su da kuma motocin su yayin da jirgi mai saukar ungulu da jami'an kwantar da tarzoma da mutanen masu zaman kansu sune suka bada gudunmawa wajen gudanar aikin ceton.Yace sai dai wannan ambaliyar tayi dalilin mutuwar mutane 3 kana mutum guda ya bata har zuwa tsakiyar ranar jiya Lahadi ba a samu ganin sa ba.

Kamar yadda hukumar kula da yanayi suka ce, anyi ruwan sama a wannan shiyyar da aka yi ambaliyar a jihar ta Louisiana da ya kai tsawon santimita 50, hukumar tace ko kafin a samu ambaliyar sai da ta fitar da sanarwan ranar talata cewa za ayi ambaliya wanda zai dangano daga daruruwar kilomita daga jihar Texas zuwa ta Arewacin kwarin Ohio.

Sai dai yawan wanna ambaliyar ta fi shafar tsakiyar jihar musammam babban birnin jihar Baton Rouge, abin da yasa hatta gwamnan shi da iyalan sa tilas suka bar gidan gwamnati.

Gwamnan yace jihar bata da karfin shawo kan wannan matsalar ita kadai don haka ya bukaci jama'ar jihar da suyi hakuri domin ko ya bukaci hukumar kula da bada agajin gaggawa ta gwamnatin tarayya da ta sa hannu, yunkurin da zai taimaka wajen ganin an taimakawa iyalai dama wadan da suka yi hasarar dukiyoyin su.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG