Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Amince Da Hukuncin Kotun Koli – Inji Gwamnatin Abdul’aziz Yari


Gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Yari

Gwamnatin jihar Zamfara mai barin gado ta Abdul’aziz Yari ta ce ta amince da sakamakon hukuncin kotun koli da ya aiyana kuri’un ta a matsayin marar sa amfani.

A sanarwa daga mai ba wa gwamnan shawara kan labaru Ibrahim Dosara, gwamnatin ta ce ta yi bakin kokarin samun nasara har matakin karshe amma Allah bai nufa ba don haka ta dau hukuncin kamar yadda Allah ya hukunta.

Hakanan gwamna Yari ya bukaci al’ummar jihar su kwantar da hankali da kuma umurtar jami’an tsaro su dage ga tsaron lafiya da dukiyar al’ummar jihar.

Za a rantsar da Bello Matawalle na PDP ranar laraba 29 ga watan nan a Gusau a matsayin gwamnan da zai karbi mulki don maye gurbin Yari da zai kammala wa’adi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG