Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Ga Masifa, Mun Ga Mutuwa, Amma Allah Ya Kubutar Da Ni


Wani soja yana gadi a kofar wani barikin soja a Maiduguri

Wani matashin da jami'an tsaro suka kama a Maiduguri suka tsare na kwanaki da dama a barikin Giwa, ya bayyana yadda rayuwa ta kasance masa, da kuma wadanda ba su ci sa'a ba suka gamu da ajali.

Wani matashin da jami'an tsaro suka kama suka kulle na tsawon wasu kwanaki a barikin soja na Giwa a Maiduguri, ya bayyana irin ukubar da ya sha da wadda ya ganewa idanunsa a lokacin da yake tsare da kuma yadda Allah Ya kwace shi da rai.

Ga irin bayanin da wannan matashi yayi a tattaunawarsa da wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu:

“Eh to, muna cikin gida ne muna kwance da asuba, suka zo suka kame mu, ba mu san abinda muka yi ba. Shi ne aka kai mu cikin New Prison, aka yi screening namu, mu 84, aka samu cikin J5, aka kai mu barack. Da (muka) je ma mutane 8 ba rai, har akwai wani malamin makarantar Arabic na Ngala, yana ta cewa ni lecturer ne, ba su yarda ba kawai, suka harbe shi ya mutu."

"Sun yi mana jerin ice a motar, wannan a kan wannan, da aka je suka fara dukanmu. Aka jefa mu a cell, mutum ma ba zai iya kwanciya ba sai dai ya zauna."

"Matan sojojin su na kawo mana tallar kayayyaki, kamar kuli-kuli, gyada, kosai, muna saya a dole don maganin yunwa. Ana ba mu abinci sau biyu a rana, kamar da karfe 10 na safe da kuma karfe 4 na yamma. Da ma wani soja yace mana mu shiga da kudinmu watakila zai yi mana amfani."

"Nayi kwana 6 a bariki. Mu 1,700 da wani abu ne a cikin cell namu wanda ake kira “Luxurious Cell.” A kullum mutane 20 zuwa 30 su na mutuwa a cikin cell din. Mu ake sanyawa mu dauki gawarwakin mu fitar waje mu ajiye. Kamar da yamma motocin ambulance na soja sukan zo su kwashe su, su zuba wani abu a kai su tafi da sho ko general hospital ko wani wuri ba mu sani ba. Mutane kamar 100 suka mutu a lokacin da nake can."

"Akwai kuma wani cell da ake kira Abuja Cell da ake cewa na masu kudi a hannu ne, amma shi bambancinsa da namu fanka ne kawai da yake da shi. Akwai kamar mutane 800 a cikinsa shi kuma. Su Su na samun ruwa, kuma akwai wani ma'aikaci a wurin idan an kawo musu wani abu daga gida zai taimaka yana rarraba musu."

"Dakin da aka sanya mu ciki kamar aji ne na makarantar firamare, babu wurin da mutum zai iya kwanciya sai dai zama, dare da rana."

"Idan mutum yayi wani abu, sai a fita da shi waje tsakar rana a daure shi a jikin injin markade, wani ma a nan zai mutu. Wasu kuma hauka ma suke yi a saboda tsabar tunani. Tun zuwanmu, wani yayi mana nasiha kan mu guji tunani don muna iya samun tabuwar hankali."

"Akwai wani rami mai duhu inda ake saka mutumin da ake zaton yana da alaka da Boko Haram. Ana kawo wanda aka san dan Boko Haram ne sai a ce ko ka san shi, in ka ce eeh sai a tafi da kai wannan ramin mai duhu. Wasu idan sun fito sukan makance don zaman da suka yi a cikin duhu na kwana da kwanaki. Wasu in sun ci sa'a sukan je asibiti suyi jinya idanunsu ya komo daga baya."

"Shawarar da zan bayar, a kawo yaran nan 'yan gora (Civilina JTF) su binciki wadanda aka tsare, idan akwai dan Boko Haram a tsare shi, wanda ba ya da laifi a sake shi. Amma duk tsawon zama na a can, ban taba jin an ce a dauki wani a kai shi kotu ba. Ba a kuma kira mu domin yi mana tambayoyi ba, tun da aka tambayi sunayenmu muka fada, aka yi mana duka, babu wani abu.”

Wakilinmu dai bai samu jin martanin hukumomin soja game da wannan zargin ba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:36 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG