Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Karbe Ikon Sansanin Boko Haram Da Ke Sambisa - Buhari


Dakarun Najeriya suna kallon wasu bama-bamai hadin gida da su ka tsinta a dajin Sambisa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce a yau Asabar, dakarun kasar sun karbe ikon wani sansanin kungiyar Boko Haram da ke cikin dajin Sambisa, wanda ya kasance tunga ga mayakan.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce kwace wannan sansani mai suna Camp Zero, wani sabon babi ne a yunkurin da ake yi na murkushe mayakan kungiyar.

Mayakan na Boko Haram mamaye dajin na Sambisa mai girman kilomita 1,300 da ke arewa maso gabashin jihar Borno.

Sai dai sanarwa ba ta ce komai ba dangane da makomar shugaban kungiyar Abubakar Shekau.

A ‘yan kwanakin nan kungiyar ta Boko Haram ta zafafa hare-harenta, bayan wasu watannin da aka kwashe ba a ji duriyarta ba.

Wannan yaki na Boko Haram ya doshi kusan shekaru bakwai ana yi, wanda ya halaka mutane sama da dubu ashirin.

XS
SM
MD
LG