Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Samu Gagarumar Galaba Akan ‘Yan fashin Dajin Zamfara – Dakarun Najeriya


Sojojin Najeriya a wani aikin sintiri da suka yi (Facebook/ Nigerian Army)

Rundunar sojojin Najeriya ta yi ikirarin kashe ‘yan bindiga da dama a yankin Talata Mafara da ke jihar Zamfara.

Zamfara na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin kasar da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.

“Yayin da take aikin sintiri, an kai wa rundunar sojin Najeriya ta 8 hari a yankin kauyukan Mayanchi-Dogo Karfe da Fagantama da ke karamar hukumar Talata Mafara.

“A mummunar arangamar da ta biyo baya, mun yi galaba akan ‘yan bindigar, hakan ya kai ga kashe da dama daga cikinsu. Sannan dakarunmu sun kwato bindiga kirar PKT da tarin harsashai da babur daya.” In ji wata sanarwa da Darektan yada labaran sojojin Najeriya Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Asabar.

Karin bayani akan: Onyema Nwachukwu, Zamfara, ‘yan bindiga, sojojin, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Kazalika sanarwar ta kara da cewa, sojojin Najeriyar sun yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga biyar a wata musayar wuta da aka yi a kauyen Bingi da ke karamar hukumar Bungudu a jihar ta Zamfara.

“Hakan ya sa ‘yan bindigar suka tarwatse saboda an jittaka da dama daga cikinsu, mun kwato bindigar kirar AK-47, babur daya da wayoyin salula uku daga hannun bat agarin.”

'Yan fashin daji sun kwashe shekaru da dama suna addabar yankin jihar ta Zamfara inda sukan saci dabbobi, su yi garkuwa da mutane su kuma kashe mutane a yankin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG