Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Wahala Matuka - Pep Guardiola


Mai horar da 'yan wasan Manchester City, Pep Guardiola (AP)
Mai horar da 'yan wasan Manchester City, Pep Guardiola (AP)

Guardiola ya bayyana hakan ne bayan da aka tashi a wasan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce sun wahala sosai a wasan da suka kara da Real Madrid a zagaye na biyu na semi-final a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

Guardiola ya bayyana hakan ne bayan da aka tashi a wasan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

“Wasan ya ba mu wahala, babu wanda zai musanta hakan.” In ji Guardiola.

Real Madrid ta doke Manchester City a zagaye na biyu a wasan semi-finals a gasar cin kofin ta Champions League a ranar Laraba

Hakan na nufin Real ce za ta hadu da Liverpool a wasan karshe na gasar ta UEFA.

An tashi a wasan ne da ci 3-1 inda dan wasan City Mahrez ya zura kwallon farko a minti na 73 a minti a ragar Real.

Sai dai Real ta yi kukan kura ta farke kwallon farko ta kuma kara wasu kwallaye biyu.

Dan wasan Madrid Rodrygo ne ya zura duka kwallayen biyun farko a minti na 90 da kuma 90+1.

Sai Kareem Benzema ya ci kwallo ta uku a bugun fenariti da Real ta samu.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG