Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Goyon Bayan Yunkurin Sulhu Da Sheikh Gumi Ke Yi -CNG


Hdakar Kungiyoyin Matasan Arewa

Hadakar kungiyoyin arewa ta sake jaddada goyon bayanta ga yunkurin sulhunta rikici tsakanin gwamnati da 'yan bindiga da Sheikh Gumi ke yi.

Duk da yake Kungiyar Dattawan Arewa ta fito karara ta nisanta kan ta da ziyarce-ziyarcen da malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad ke yi a sansanonin 'yan bindiga da suna sulhu, wata hadakar kungiyoyin arewa wato Coalition of Northern Groups ta sake jaddada goyon bayanta ga yunkurin na Sheikh Gumi.

Taron Hadakar Kungiyoyin Arewa
Taron Hadakar Kungiyoyin Arewa

Shugaban kwamitin Amintattu na gamayyar kungiyoyin Arewa, Nastura Ashir Shariff, ya bayyana cewa a yanzu kamata yayi a karfafa nemo mafita kan matsalar cikin gaggauwa domin kaucewa yiyuwar maimaita matsalar Boko Haram da aka kwashe sama da shekaru 10 ana fama da ita.

Nastura Ashir ya kara da cewa matsalar Boko Haram da ta ki ci ta ki cinyewa, sakamako ne yadda wasu ‘yan siyasa da wasu ‘yan kudancin Najeriya da kungiyoyin addini suka yi ta rigima a lokacin, bayan da hadakar kungiyoyin Arewa ta bada shawarar a zauna a kan teburin sulhu da ‘yan ta’addar.

Hadakar kungiyoyin ta bayyana ra'ayin nata ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a birnin tarayya Abuja, tana mai cewa ba ta fatan sake aukuwar irin abin da ya faru da kungiyar Boko Haram ya zama makomar ‘yan bindiga dadi a Arewa maso Yamma, wadda kankanuwar fitina ce da za a iya magancewa.

Hdakar Kungiyoyin Matasan Arewa
Hdakar Kungiyoyin Matasan Arewa

"Makiyaya ne a ka zalunta ta hanyar kirkiro barayin shanu, aka yi ta kwace musu shanu da hadin gwiwar wasu hukukomi har ya kai ga suka dauki makamai, lamarin da ya rikice zuwa ga rikicin manoma da makiyaya da ya ki ci ya ki cinyewa, kuma tun da aka gano matsalar, a sulhunta su da mutanen garuruwa su karbe su, wadanda suka yarda su ajiye makaman su" in ji shugaban hadakar, Nastura ashir.

Ya kara da cewa kungiyar ta yi Allah wadai da wasu da ke yin tir da aikin sulhu da Sheikh Gumi ke jagoranta, inda Nastura ke cewa, suna yi ne da zummar karban mulki a shekarar 2023 sakamakon yadda suke da mummunar manufa kan arewa, kuma "ba za su samu nasara ba saboda al’umman arewa ba za su dau hanyar ramuwar gayya ba."

Daga karshe dai Nastura Ashir Shariff ya ce "idan raba kasa zai sa a zauna lafiya gara a raba ta a ba wa kowa hakkinsa a maimakon a yi ta kashe mutanen arewa a ce a yi shiru don kasa ta zauna lafiya", tare da yin kira ga gwamnonin da ba su yarda da sulhu ba da su yi domin zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG