Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Son Dinke Duk Wata Baraka A APC - Mai Mala Buni


Gwamna Mai Mala Buni

Sabon shugaban riko na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Mai Mala Buni, ya sha alwashin dinke duk wata baraka, da kuma sake gina jam'iyyar wadda ta yi fama da rikicin shugabanci.

Jam'iyyar ta APC ta kwashe tsawon lokaci tana fama da matsalar cikin gida, da suka hada har da rikicin shugabanci, lamarin da ya sa wasu bangarori zuwa kotu.

A 'yan makonnin baya wata kotu a birnin tarayya Abuja, ta tabbatar da dakatar da shugaban jam'iyyar Adams Aliyu Oshiomhole, inda daga baya aka nada gwamnan jihar Yobe Alh. Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko.

Adams Oshiomhole
Adams Oshiomhole

A wata tattaunawa da Muryar Amurka ta yi da sabon shugaban, ya musanta da'awar da wasu ke yi na cewar shugaba Buhari ne sanadi na duk wata matsala a jam'iyyar.

"A duk lokacin da ka ji an yi maganar gyara, to babu shakka akwai barna" wannan shi ya sa aka dauki matakan kawo karshen matsalolin. Shugabanin baya sun yi ba daidai ba, amma yanzu mu na sa ran kawo karshen duk wata matsalar cikin gida a tsakanin mu," a cewar Gwamna Mai Mala.

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Mai Mala, ya kara da cewa "tun a shekarar 2013, lokacin gamin gambizar jam'iyyu, aka yi wa jam'iyyar ta APC hasashen fuskantar matsala, don haka wannan ba wani sabon abu ba ne a kowace jam'iyyar ta fuskanci rikicin cikin gida."

"Kada kuma a manta tsohon mataimakin shugaban kasa Alh. Atiku Abubakar, ya taba barin jam'iyya da gwamna daya, amma hakan bai sa jam'iyyar PDP kasa cin zabe ba, wannan ya sa mu ke da kwarin gwiwar cewa insha Allah za mu yi nasara a gaba."

A karshe dai Gwamna Mai Mala ya nuna rashin damuwarsa da zabe a yanzu duba da yadda ake da shekaru akalla uku kafin lokacin.

Saurari cikakken hirar Muryar Amurka da Gwamna Mai Mala cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:02 0:00


  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG