Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muryar Amurka Na Binciken Zargin Cewa Wani Dan Jaridarta Yayi Kalamun Batanci a Kafar Internet


Amanda Bennett babbar daraktar VOA
Amanda Bennett babbar daraktar VOA

Muryar Amurka na binciken zargin cewa wani dan jaridar kamfanin ya rubuta wani kalami na nuna bambancin launin fata da raina jinsi da kuma cin mutuncin ‘yan luwadi a kafar ‘internet,’ inda ya yi amfani da wani suna na bogi. Tuni aka tura dan jaridan hutun dole a yayin da ake cigaba da bincike.

Da ta ke tofa albarkacin bakinta game da binciken, Daraktar Gidan Rediyon Muryar Amurka Amanda Bennett, ta ce, “Sam Muryar Amurka ba za ta lamunta ba da maganganu masu nasaba da nuna bambancin launin fata da rainin jinsi da son zuciya irin na siyasa ba. Manufofin Muryar Amirka ko kuma na gwamnatin Amurka sun nuna karara cewa wannan halin ba abin yadda dashi ba ne.”

Amanda Bennett yayinda take jawabi
Amanda Bennett yayinda take jawabi

Muryar Amurka kafar labarai ce ta kasa da kasa da gwamnatin Amurka ta kafa; kuma ta na yada shirye-shirye na tsawon sa’o’i 1,500 a duk mako ga masu sauraronta masu yawan miliyan 236 a duk fadin duniya. Dokar da ta tanadi kafar labaran ta nemi da ta kasance mai gaskiya da kyakkyawar manufa da saukin fahimta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG