Accessibility links

Yayin da kungiyar hadin kan 'yan arewa ta yi taron salla Mataimaki Tom Maiyashi ya ce idan ana so a zauna lafiya to a kula da irin mutanen da ake zama shugabanni.

Mr. Mataimaki Tom Maiyashi masanin ilimin zamani ya ce idan ana son fita daga halin da kasar ta samu kanta to dole ne mutane su lura da irin shugabannin da suke zaba lokacin zabe.

Mr Maiyashi yana cikin kungiyar hadin kan 'yan arewa kuma ita ce ta shirya hidimar bikin salla wanda ya kunshi Musulmai da Krista a Kaduna. Ya ce idan ana son shugabanci na gari to dole a dinga nazarin wanene za'a zaba. Ya ce idan shugabanci ana yi ne saboda al'umma to a dubi abubuwan da suka damu al'umma a kuma maganta masa su.

A nashi jawabin Shekh Lurwanu Mohammad Gwangola ya ce da ana samun shugabanni masu adalci to da babu kasar da zata fi kasar Najeriya arziki domin irin albarkatun da Allah Ya ba kasar.Ya ce shugabanninmu daga kowace bangare suna tara dukiyar al'umma ta zama tasu da iyalansu kawai. Ya ce shugaban da ya yi hakan ya jawo wa mutanensa wata masiba da bata da iyaka.

Shi kuma Bishop Samuel Usman cewa ya yi wasu mutane ne ke son ruda 'yan Njeriya da maganar ban-bancin addini. Ya ce idan da Allah ya so duk a zama Musulmai da babu wani addini daban. Haka inda Allah ya so duk mu zama Krista da babu wani addini daban. Ya ce kana masu rudinmu da addini basu da gaskiya. Mazalunta ne. Suna fakewa ne da guzuma su harbi karzana.

Daya daga cikin mahalartan taron Manjo Yahaya Shinko ya ce dama maganar ban-bancen addini kutsowa aka yi da ita. Ya ce idan ana bin siyasar kasar nan an dauko abin mataki-mataki ne. An fara da kawo ban-bancin bangaranci amma bai ci nasara ba. Sai kuma aka yi anfani da kawo ban-bancin kabila wannan ma bai yi nasara ba.Sai suka kawo na addini shi ne kuma ya kawo mu halin da muke ciki yanzu.

Daga karshe shugaban kungiyar Alhaji Adamu Aliyu ya ce kungiyarsu ta hadin kan Musulmai da Krista ce. Dalilin taron shi ne mabiya addinan biyu su taru su taya juna murnar kawo karshen azumi cikin lumana da nuna kauna ma juna. Don haka a kowane lokaci a shirye suke su kira irin wannan taron.

Isah Lawal Ikara nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG