Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmai Da Kristoci Sun Yi Addu’o’i Na Musamman a Taraba


Musulmai Da Krista Sun Yi Addu'o'i Na Musamman a Taraba
Musulmai Da Krista Sun Yi Addu'o'i Na Musamman a Taraba

Dubban jama’a ne Musulmi da Kristoci suka fito kwansu da kwarkwata a garin Jalingo, dake zama fadar jihar Taraba, domin gabatar da addu'o'i na musamman don rokon Allah ya bai wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, lafiya.

Idan dai ba’a mance ba, a ranar 19 ga watan Janairun da ya wuce ne dai shugaba Buhari ya tafi hutu tare da ganin likita a Birtaniya, to amma kuma daga bisani sai shugaba Buharin ya sake aika wa Majalisar Dokokin kasar takardar neman tsawaita hutun da zummar kammala gwaje-gwajen lafiyarsa.

Tun wannan lokacin ne aka fara gudanar da addu’o’i a Majami’ai da Masallatai don nema wa shugaban lafiya.

Da suke gabatar da addu’o’in Evangelist John Adamu da Sheikh Aliyu Babando da kuma wakilin kungiyar CAN, Rev. Baba Yerima, sun yi addu’ar neman Allah ya baiwa shugaban kasa lafiya da kuma kawo daidaito a jihar Taraba.

Shima da yake jawabinsa a wajen gangamin addu’ar Galadiman Muri, Alhaji Tukur Abba Tukur, ya yaba da yadda jama’a suka fito don gudanar da wannan addu’a

Musulmai Da Krista Sun Yi Addu'o'i Na Musamman a Taraba
Musulmai Da Krista Sun Yi Addu'o'i Na Musamman a Taraba

Shi kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar, Hassan Jika Ardo, yace ya zama dole ‘yan Najeriya su tashi tsaye don yiwa shugaba Buhari addu’a, idan aka yi la’akari da irin nasarar da aka fara samu kasar.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG