Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutan Vietnam Sun Fusata da China


Daruruwan mutane ne Lahadinnan, suka yi dafifi da cin-cirindo a wajen kofar shiga ofishin jakadancin kasar China dake Vietnam, suna zanga-zangar nuna rashin amincewa da barin China yin musayar rijiyoyin mai a yankin ruwan tekun da ake takaddama kansu a kudancin ruwan tekun China.

An tura jami’an tsaro cikin farin kaya wasu kuma cikin kaki suna zuba ido domin hana karya dokar da aka kafa wajen hana masu zanga-zangar tsallaka titi su kutsa yankin da ofishin jakadancin yake.

An bayyana wannan zanga-zangar a zaman daya daga ckin mafi karfin da aka taba yi inda masu adawa da manufofin China ke zanga-zanga a fili suna daga tuta tare da zage-zagen batunci ga hukumomin China.

Idan za’a tuna, duk abinda ya janyo hakan shine tura jiragen ruwan jigilar man da Vietnam tayi zuwa rijiyoyin man gabar ruwan tekun China da Vietnam tayi a ran daya ga watan nan na Mayu, amma basu sami nasarar kaucewa wani kambun jiragen ruwan yakin da China tayi ba domin nuna rashin amincewarta.
XS
SM
MD
LG