Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ba A San Abinda Ya Samu Mutane 1000 A Girgizar Kasar Nepal Ba


Wani gini a Nepal kenan da ya ruguje sanadiyyar girgizar kasar.
Wani gini a Nepal kenan da ya ruguje sanadiyyar girgizar kasar.

Mako daya bayan gagarumar girgizar kasa mai nauyi maki 7.8 a kasar Nepal, jami’ai sun ce har yanzu ba a ga dubban mutane ba ciki har da ‘yan kasashen Turai a kalla guda 1000.

A jiya hukumonin Nepal sun bayyana cewa yawan mutanen da suka halaka a girgizar kasar ya haura 6,600 a tsakanin ciki da wajen birnin Kathmandu. Sai dai jami’an sun ce suna sa ran ceto wasu da ka iya samun tsira a gagarumin binciken da ake na wadanda abin ya ritsa da su.

Wadanda a yanzu suka sami tsira suna kira ga gwamnati da sauran kungiyoyin agaji da su taimaka musu da gaggawa don samun abinci da ruwan sha da sauran ababen tallafi gare su da a yanzu suke a sarari sakamakon rasa muhallansu.

A Kathmandun dai ga alama al’amura sun fara dawowa daidai har masu saye da sayarwa sun fara kasuwancinsu sannan wasu sun nade tantinan da suke kwana sun shiga daga cikin gidajensu, amma warin gawarwaki ya hana da dama komawa gidajensu.

A wata ziyarar kwanaki 3 da shugabar kula da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta kai yanki ta ce kayayyakin agaji sun fara samuwa a yanki tare da yin kira ga duniya data taimaka don samun karuwar kayan agaji ga jama’ar kasar.

Gwamnatin Nepal tana bawa iyalan wadanda suka rasa ransu Dalar Amurka 1000 da kuma Dala 400 don binne mamatan. Majalisar dinkin duniya tace mutane kimanin Miliyan 8 wannan bala’in ya shafa sannan Miliyan 2 sun rasa muhallansu.

XS
SM
MD
LG