Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 13 Sun Mutu A Hadarin Jirgin Mexico


Tarkacen jirgin da ya fadi

A wani al'amari mai kama da bala'i kan bala'i, wani jirgin yakin Mexico ya yi hadari yayin shawagin duba barnar da girgizar kasa ta yi; ya kashe mutane 13.

Wani jirgin yaki mai saukar ungulu da ke dauke da wasu jami’an gwamnatin Mexico ya fadi jiya Jumma’a a yayin da su ke dudduba irin barnar da girgizar kasar da ta auku ta yi. Jirgin ya kashe wasu mutane biyu da ke kasa.

Jirgin na dauke ne da Ministan Cikin Gidan Mexico Alfonso Navarrete Prida da kuma gwamnan jahar Oaxaca Alejandro Murat, wadanda ba su ji wani mummunan rauni ba.

Girgizar kasar ta auku ne a Kudancin Mexico jiya Jumma’a, inda ta yi wata ‘yar barna a jahar Oaxaca, to amma nan take babu wani rahoton mutuwa ko jin rauni.

Cibiyar binciken karkshin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar na da karfin 7.2 a ma’aunin girgizar kasa kuma ta samo asali ne a wani yankin karkara na kudancin jahar ta Oaxaca daura da gabar Tekun Pacific da kuma kan iyakar jahar Guerrero.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG