Accessibility links

Mutane 16 Sun Mutu, da Yawa Sun Ji Ciwo, Gidaje Fiye da 20 Sun Kone Kurmus a Kauyen Shonon, Jahar Filato


Irin bannar da ta wakana bayan harin.

Wasu maharan da ba a san ko su waye ba ne suka aikata wannan ta'asa.

Wakiliyar Sashen Hausa a jahar Filato Zainab Babaji ta aiko da rahoton cewa rundunar 'yan sandan jahar ta tabbatar da cewa wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan kauyen Shonon a karamar hukumar Riyom, kuma rundunar ta tabbatar da konewar gidaje fiye da ishirin, da mutuwar mutane goma sha shida da kuma raunata wasu da dama da ke kwance a asibiti kamar yadda za ku ji karin bayani daga bakin kwamishinan 'yan samdan jahar Filato Chris Olakpe:

XS
SM
MD
LG