Accessibility links

Tashin Hankalin Janhuriyar Afirka ta Tsakiya Ya Rutsa da Wasu 'Yan Nijar

  • Ibrahim Garba

Sojojin kasar Faransa kenan ke sintiri a birnin Bangui

Wasu 'yan Janhuriyar Nijar sun sami kansu cikin tsaka mai wuya dangane da rikicin kabilanci da addinin da ke faruwa a Janhuriyar Afirka ta Tsakiya

Yakin da ake yi a Janhuriyar Afirka ta Tsakiya ya rutsa da daruruwan 'yan Nijar da sauran 'yan wasu kasashen Afirka da ke zama a Bangui babban birnin kasar da kuma wasu biranen kasar.

Wani mazaunin birnin Bangui mai suna Nuhu Abubakar ya shaida wa wakilinmu a Janhuriyar Nijar Abdullahi Mammane Ahmadu cewa rikicin kabilanci da addinin ya sa Hausawa da Fulani da Larabawa sun taru wuri guda saboda kar wani ya abko masu. Malam Nuhu ya ce shekaran jiya an baza sojojin kasar to amma tunda sojojin Faransa da na "Alliance Farancaise" su ka iso sai sojojin kasar su ka kau.

Shi kuwa wani dan rajin kare hakkin dan adam mai suna Mustafa Kadi kira ya yi ga gwamnatin Janhuriyar Nijar da Majalisar Dinkin Duniya da su kai dauki don ceto mutanen da yakin ya rutsa da su - musamman ma wadanda ba hannunsu ciki.

XS
SM
MD
LG