Accessibility links

Mutane 17 sun rasu a wata fashewa a Iran

  • Ibrahim Garba

Hayaki ke tashi daga ma'adanar makaman Iran da ta yi bindiga

Hukumomi a kasar Iran sun ce wata babbar fashewar

Hukumomi a kasar Iran sun ce wata babbar fashewar da ta auku a wata ma’adanar kayan yaki da ke yamma da birnin Tehran ta kashe a kalla 17 daga cikin dogarawan tsaron kasar na musamman.

Kafafen yada labaran gwamnati sun ce wani babban kwamandan dogarawan yam utu cikin hatsarin. A kalla wasu kuma 16 sun sami raunuka wasunsu ma munana.

Mai magana da dakarun na musamman Ramazan Sharif y ace bincike na farko ya nuna cewa fashewar ta auku ne lokacin da sojoji ke jigilar wasu kayan yaki a wurin. Masu binceken sun ce bas u tsammanin akwai wata makarkashiya.

Wannan gagarumar karar ta lalata gine-ginen da ke kusa da wurin kuma har ta jijjiga sassan babban birnin kasar mai tazarar kilomita 40 daga wurin.

XS
SM
MD
LG