Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kasashen Larabawa na gab da dakatar da Siriya


Masu zanga zanga a Siriya

Jiya Asabar kungiyar kasashen Larabawa ta kada kuri’ar amincewa

Jiya Asabar kungiyar kasashen Larabawa ta kada kuri’ar amincewa da dakatar da kasar Syria daga gudanar da harkoki a kungiyar, har sai lokacin da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta fara aiwatar da yarjajjeniyar zaman lafiya, ta kawo karshen gallazawa ‘yan tawayen.

A wani jawabin da Firayim Ministan Qatar, kuma shugaban kungiyar ta kasashen Larabawa Hamad bin Jassim al-Thani ya karanta bayan taron gaggawan da su ka yi a birnin al-Khahira, y ace Syria za ta cigaba da zama mamban wannan kungiya ta kasashe 12 to amman fa dole ne Syriar ta janye dakarunta daga titunan kasar, ta fara tattaunawa da ‘yan tawaye ta kuma sake fursunonin siyasa. Idan ba haka ba to dakatarwar za ta fara aiki ranar Laraba.

Kungiyar ta kuma yi kira ga dukkannin kasashen Larabawa su janye jakadunsu daga Syria su kuma dubi yiwuwar kakaba wa kasar takunkumin tattalin arziki.

Jakadan Syia a Kungiyar Yousef Ahmed, yay i watsi da wannan matsayin da cewa bai bisa ka’ida kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin kungiyar. Y ace gwamnatinsu ta dukufa wajen aiwatar da yarjajjeniyar zaman lafiyar da kungiyar ta cimma a farkon wannan watan.

A birnin Dimaskus daruruwan masu zanga-zanga cikin bacin rai sun far ma gine-ginen jakadancin Saudiyya da na Qatar don nuna bacin ransu da matakin da kungiyar ta kasashen Larabawa ta dauka.

Wani ayarin masu zanga-zangar ya yi ta ruwan duwatsu kan ginin jakadancin Saudiyya tare da farfasa tagogi. Wasu daga cikin masu zanga-zangar kai ga kutsawa cikin harabar ginin su ka wargaza abubuwan ciki.

Wannan gungun mutanen sun kuma kutsa ta mashigar ofishin jakadancin Qatar suna ta ambaton kalaman batunci ga kasar Qatar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG