Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 18 Suka Mutu A Tarzomar kasar Malawi


Dan zanga-zanga a Lilongwe, babban birnin malawi, laraba 20 Yuli, 2011

Gwamnati ta ce adadin wadanda suka mutu a arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga yanzu ya kai akalla 18

A yanzu dai, gwamnatin Malawi ta ce mutane akalla 18 ne aka kashe a arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati kama daga jiya laraba.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Malawi ita ce ta bayyana karin yawan wadanda aka kashe yau alhamis, jim kadan a bayan da shugaba Bingu Wa Mutharika yayi jawabi ta rediyo ga al’ummar kasar yana rokon a kwantar da hankula. Shugaban yace a shirye yake ya zauna ya tattauna da ‘yan adawa.

Mummunar tarzoma ta barke jiya laraba a birane uku da suka fi girma a kasar, watau Blantyre da Mzuzu da kuma Lilongwe babban birnin kasar. Jami’ai suka ce an yi mace-macen ne a birnin Mzuzu a lokacin da ‘yan sanda suka kara da masu zanga-zanga.

Shaidu sun ce ‘yan tarzoma sun fasa kantuna su na kwashe kayayyaki tare da cunna musu wuta a lokacin zanga-zangar, kuma ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa.

Masu zanga-zangar su na nuna rashin jin dadinsu ne da karancin man fetur, da hauhawar farashin kayayyaki da kuma yadda ake take hakkin jama’a a wannan kasa dake yankin kudancin Afirka.

XS
SM
MD
LG