Accessibility links

Zancen Tattaunawa Kan Saukar Gaddafi Ba Ta Taso Ba a Cewar Firayim Minista

  • Aliyu Mustapha

Dakarun 'yan tawayen Indiya

Firayim Ministan Libya yace sam, ba wata tattaunawa da zasuyi da kowa a duniya gameda wai

Firayim Ministan Libya yace sam, ba wata tattaunawa da zasuyi da kowa a duniya gameda wai ko shugaban Libya Muammar Ghadafi ya zauna a kasar ko ya barta, yaje wani gun.

Haka kuma Farayim Minista din, Al-Ba ghdadi al-Mahmoudi ya fada a yau cewa ba wata tataunawar arziki da zasuyi da kowa akan rikicin siyasar kasar muddin ba a ja burki ga abinda ya kira “gallazawar NATO” ba.

Firayim Ministan yana wannan kalamin ne jim kadan bayan ganawarsa da wani manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya (Abdul Elah al-Kahtib) wanda shi kuma jiya-jiya ya gama saduwa da jagabannin ‘yantawayen Libya din.

sai dai, da take maida murtani ga wadanan kalaman a birnin Brussels. wata mai magana da yawun NATO tace za’a ci gaba da fatattakar da sojan NATO ke yiwa Libya har zuwa lokacinda bukatar yin hakan ta kau.

XS
SM
MD
LG