Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 22 Sun Mutu Sanadiyar Fashewar Bam A Siriya


Akasarin wadanda fashewar bam din ya shafa 'yan Shi'a ne wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa Aleppo.

An samu labaran cewa ‘yan kasar Syria da yawa sun rasa rayukan su wasu kuma sun ji raunuka sakamakon wani bam da ya fashe a yau Asabar a jerin motocin da ke dauke da duban wadanda ake kwashewa.

Kungiyar dake sa ido kan harkokin hakkin dan adam ta Syria, tace fashewar Bam din ta shafi jerin gwanon akasarin ‘Yan shi’a magidanta ne. Kungiyar mutanen na tafiya ne zuwa Aleppo daga wasu kauyukan Fuaa da kuma Kafraya, bayan sun cimma yarjejeniyar kwashesu da subar gidajen su.

Gidan Talabijin na Syria ya bada Rahoton kimanin mutane 22 ne suka mutu a sakamakon fashewar Bam din a garin Rashidin. Kungiyar saido kan hakkokin dan adam ta Birtaniya dake Syria ta ce adadin wadanda suka mutum yakai 24 kuma Fashewar Bam din ta afkune sakamakon Bam din da aka saka a mota.

Dubbban ‘yan kasar Syria dake guduwa daga garuruwa hudu da aka mamaye sun yi cirko cirko akan hanya a wajen birnin Aleppo rana guda bayan barin gidajen su.

‘Yan tawayen kasar Syria dai su suka rufe hanyoyin wadanda suka ce an karya kaidojin da aka shardanta na kwashe mutanen tsakanin Iran da Qatar a watan da ya gabata ba ida suba, kamar yadda Kungiyar da ke sa’ido akan harkokin hakkin dan Adam a Syria ta fada.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG