Accessibility links

Kimanin mutane dubu ashirin da biyar ne tare da tsohon ministan yada labarai Ikra Aliyu suka canza sheka daga jamiyar PDP zuwa ta APC a wani gangami a Gusau.

Tsohon ministan yada labarai a lokacin shugabancin marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua, Ikra Aliyu Bilbis ya canza sheka daga jamiyar PDP mai mulkin Najeriya zuwa jam'iyyar adawa ta APC tare da magoya bayansa dama wasu jiga-jigan jamiyar PDP a matakin jihar ta Zamfara.

Tsohon ministan wanda tun a shekarata 1999 yake cikin jamiyar PDP ya bayyana dalilansa na canja shekar a gaban tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da gwamnonin Zamfara, Sokoto da Adamawa, a wani babban gangamin APC a birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Aliyu Bilbis yace “mun fi dubu kusan ashirin da biyar yanzu a wannan wuri wanda muka yarda muka amince shiga wannan jamiyyar mai albarka.”

Mr. Bilbis ya kara da cewa “makasudin shigar mu jamiyar APC kowa ya san abunda ke faruwa a kasan nan, mu daina yaudaran kanmu, mu daina gayawa kanmu karya. Gaskiya tazo yanzu lokacin da ‘yan najeriya zasu canja gwamnati da mulki na gaskiya na adalci, kowa ya san ni cikaken dan adawa ne a wannan jihar yau tarihi ya nuna.”

Gwamnar jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar, na ganin wannan babban kamu ne da jamiyar sa ta APC tayi, amma yace “wannan somin tabi ne, duk wadanda suka yi ministoci inda aka fito yau muna tare dasu a nan wandanda basu nan a basu lokaci kadan suma suna tafe.”

Shi kuwa Atiku Abubakar cewa yayi ”randa aka ce makwabci baya tare da kai, Sokoto, Zamfara yaya zakuyi da Kebbi? Ai a lokacin da, duka jihohin nan tare suke mai zai sa ace yau Kebbi bata cikin wannan tafiyar? Ga manyan Sokoto, ga manyan Zamfara saura ku dawo da manyan Kebbi."

Amma gwamnan jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako mai ritaya, mayar da hankali yayi akan halin da jihar ta Zamfara take ciki na kashe-kashen rayukan jama’a.

“Don Allah mutanen Zamfara, kada ku yarda kuyi fada tsakanin junanku, bare a zubda jini. Ba wani fulatani da zai kashe bahaushe, babu bahaushen da aka san ni yana kashe bafulatani. In aka yi kisa a nan to daga Abuja aka aiko su, dama Allah-Allah ake a samu muyi fada akan kabilanci, akan addini akan ina aka haife mu.

Jamiyyar PDP ita ma a kwanakin baya ta fito karara ta zargi jamiyyar APC da hura wutar tashe-tashen hakula, abinda jamiyyar ta musanta.
XS
SM
MD
LG