Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Namadi Sambo Bai Taimakawa Arewa Ba - inji Solomon Dalung


Mataimakin Shugaban Najeriya, Namadi Sambo
Mataimakin Shugaban Najeriya, Namadi Sambo

Yayin da yake mayarda martani akan kiran da wasu suke yi cewa shugaba Jonathan ya nemi wani mataimaki daga arewa a madadin Namadi Sambo, Solomon Dalung yace a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa bai taimakawa arewa ba

A wata fira da abokiyar aiki tayi da Barrister Solomon Dalung daya daga cikin 'yan kungiyar dattawan arewa, yace damuwarsu da mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo shi ne gazawarsa wurin kare arewa a gwamnatin tarayya.

Yace wadanda suke maganganu akan mataimakin shugaban kasa 'yan jam'iyyarsa ne da aka sayesu domin su bata masa suna. Domin haka shi babu ruwansa da wadannan mutanen. Ba zai shiga harakar jam'iyyarsu ba. To saidai a zaben 2015 yace ba zasu samu da sauki ba kamar yadda suka saba samu.

Namadi Sambo dan arewa ne. Shugaba ne a arewa kuma mataimakin shugaban kasa. Amma su dattawan arewa da mutanen arewa basu ji yunkurinsa ba kamar yadda suka saba gani a wurin mutumin dake rike da irin wannan mukamin. Bai yi wani motsi ba ko a ofishinsa domin a tausayawa mutanen arewa. Duk abubuwan dake faruwa kaman hare-hare bai taba cewa komi ba ko ya kai ma wadanda abun ya shafa taimako ba a matsayinsa na dan arewa kuma shugaba daga arewa. Yace su dattawan arewa damuwarsu da Namadi Sambo ke nan.

Ya cigaba da cewa Namadi Sambo na yi kamar ya juyawa arewa baya. Saboda haka idan 'yan jam'iyyarsa suna kira a cireshi maganarsu ce ta jam'iyyarsu. Ra'ayinsu ne domin lamarin kaman na 'yan fashi ne da suka fasa banki suka kwashi kudi da suka je wurin rabawa suka fara fada da junansu. A cikin fadan sai wani ya jiwa wani ciwo sai aka kwasosu zuwa caji ofis amma maimakon a tuhumesu da fashin banki sai ana tambayarsu maganar fada da suka yi. Wato an bar ainihin magana an fadawa wata daban.

Yace ko a canza mataimakin kasa ko kada a canza ba shi ne damuwarsu ba. Abun da ya kamata Namadi Sambo yayi shi ne ya dawo a matsayinsa na dan arewa ya hada kai da dattawan arewa domin a ceci arewa daga halin da take ciki yanzu. Kawo yanzu dai Namadi Sambo bai taimakawa arewa ba. Bai nuna cewa shi mutumin arewa ne ba. Bai damu da koina ba sai da Abuja kana da wucewa zuwa turai. Yakamata ya nemi yin gyara.

Ga rahoto.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG