Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 33 Ne Suka Mutu Bayan Wata Fashewa A Mahakar Ma'adanai A China


Masu aikin ceto a China
Masu aikin ceto a China

Wani gidan yada labarai na jiha a China ya rawaito cewa Mutane 33 da uku ne suka rigamu gidan gaskiya sakamakon fashewar wani abu a Ranar litinin a wata mahakar Ma’adanin Kwal dake garin Chogqing a China.

Mutane biyu ne suka tsira da rayukansu a yayin hadarin a Mahakar Ma’adadin na Kwal mallakar Jinshangou a garin Laisu. Da fari gawarwakin mutane 13 aka hako yayin da Yan agaji ke kokarin cire burbushin Fashewar, da kuma fatan samun wadan da suka tsira. Amma an gano gawarwakin ragowar da ba’a gani ba a yau Laraba.

Jami’ai sun fara bincike akan abinda ya jawo wannan mummunan fashewa da kuma jamia’amn kula da lafiya sunce, duk wanda yake da hannu acikin faruwar al’amarin zai fuskanci hukunci mai tsauri. Jami’n gundumar sun bada umarnin rufe Mahakar Ma’adanin ana Kwal ta wucin gadi a wannan yanki.

A farko farkon wannan shekarar Xianhua ta rawaito cewa Jami’an Kula da na Kasa a China sun tabbatar da Mutuwar Mutane 171 da suka afku sakamakon Hadari a Mahakar Ma’adanin kwal da kuma na Iskar Gas 45 a shekarar 2015.

XS
SM
MD
LG