Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 43 Suka Hallaka A Harin Continental Hotel A Kabul, Afghanistan


Smoke rises from a fire onboard the <em>MV X-Press Pearl</em> vessel as it sinks while being towed into deep sea off the Colombo Harbor in Sri Lanka. (Credit: Sri Lank Air Force)
Smoke rises from a fire onboard the <em>MV X-Press Pearl</em> vessel as it sinks while being towed into deep sea off the Colombo Harbor in Sri Lanka. (Credit: Sri Lank Air Force)

Sojojin gwamnatin Afghanistan sun kawo karshen harin da aka kai kan Intercontinental Hotel dake Kabul babban birnin kasar, bayan mutane 43 sun hallaka, cikinsu har da 'yan kasashen waje 14

Sojojin Gwamnatin Afghanistan sun kawo karshen kofar-ragon da aka yiwa wani babban Otel mai suna Intercontinental Hotel dake Kabul, da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da raunata wasu. Akwai ‘yan kasashen waje guda 14 da lamarin ya rutsa dasu.

Wasu 'yan jaridar Afghanistan wadanda suka ziyarci wurin jiya Lahadi sun yi amfani da shafukan sada zumunci wajen bayyana cewa sun ga gawarwaki da dama a cikin otel din. Babban gidan talabijin din Afghanistan mai suna TOLO News ya ambaci wata majiya mai tushe tana cewa harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 43.

Kamfain jirgin saman Kam Air ya bayyana cewa ma’aikatan sa 10 ne suka mutu a harin, ciki harda masu tuka jirgin sama guda 5. Mutane 2 ‘yan kasar Venezuela, da 6 ‘yan Ukraine na cikin wadanda harin ya rutsa da su.

An kai sa’o’i 14 ana Fafatawa tsakanin mayakan da jami’an tsaro. Mayakan sa kai 6 ake kyautata zaton sun kai harin. Da alama ko an kashe su cikin gumurzun ko kuma sun tarwatsa kansu da kansu.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG