Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 6 Suka Mutu A Harin Bam A Maiduguri


'Yan sanda su na gadin wata muhimmiyar hanya a Maiduguri, Jihar Borno

Akwai dan sanda daya cikin wadanda suka mutu a lokacin da dan kunar bakin wake yayi kokarin shiga hedkwatar 'yan sandan a Maiduguri

Hukumomi a Najeriya sun ce an kashe mutane akalla 6 a wani harin bam na kunar bakin wake da aka kai cikin mota a garin Maiduguri.

‘Yan sanda suka ce wannan dan kunar bakin wake ya tarwatsa motar da yake ciki jiya jumma’a a kofar hedkwatarsu. Akwai dan sanda guda daya daga cikin wadanda suka mutu, yayin da wasu mutane 7 suka ji rauni.

Wannan lamarin ya faru kwana guda a bayan da ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya shawarci dukkan Amurkawa dake cikin Maiduguri da su bar garin saboda tashin hankalin da ake ci gaba da yi.

A ranar alhamis, ofishin jakadancin yayi kashedi a game da tashin hankalin da ake ci gaba da yi a tsakanin dakarun gwamnati da abinda ta kira “tsagera na yankin” a garin Maiduguri. Ofishin jakadancin yace yayi imani wannan lamarin zai ci gaba da tabarbarewa.

Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin harin na jiya jumma’a, amma kungiyar nan ta Boko Haram ta kai ire-iren wannan harin a can baya.

Maiduguri ne cibiyar kungiyar ta Boko Haram wadda aka dora ma alhakin mutuwar daruruwan mutane a Najeriya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG