Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 11 Sun Mutu, Gidaje Kusan Miliyan Hudu Ba Su Da Wutar Lantarki A Amurka


Wata katuwar bishiya ta fado kan motar wani mutum mai suna Mike Wolfe a wani gari mai suna Falls Church a Jihar Virginia, dab da birnin Washington DC, bayan mummunan hadarin ruwan sama da iska, asabar 30 Yuni 2012.

A bayan wani hadarin ruwan sama mai tsanani tare da iska mai karfi a Washington DC da sauran yankunan gabashin Amurka

Mutane akalla 10 sun mutu, yayin da gidaje fiye da miliyan uku ba su da wutar lantarki yanzu haka a bayan da wani irin hadarin ruwan sama mai tsananin karfi da iska ya ratsa ta kan yankin gabashin Amurka jumma’a da daddare.

Wannan hadarin ya zo a daidai lokacin da ake yin wani irin zafin da ba a taba ganin irinsa ba a nan yankin na gabashin Amurka. Ruwan sama da iska sun tuge bishiyoyi, suka kwantar da wayoyin lantarki, har ma gwamnonin jihohi hudu, Ohio da Virginia da West Virginia da kuma Maryland, da kuma hukumomin nan birnin Washington Gundumar Colombia, suka ayyana kafa dokar ta baci.

Mutane 6 sun mutu a Jihar Virginia mai makwabtaka da nan Washington, biyu a Jihar New jersey, daya a Maryland daya kuma a Ohio. Akasarinsu bishiya ce ke faduwa a kansu ko gidajensu ta zamo ajalinsu.

An dauke wutar lantarki a kusan kowace gunduma a wannan yanki, yayin da jami’ai suke fadin cewa za a dauki kwanaki da dama kafin a maido da wutar ga kowa da kowa.

Daya daga cikin wadanda suka rasa wutar lantarkin su na nan babban birnin Amurka da kuma garuruwan dake kewaye da shi, ciki har da garin Brandywine a Jihar Maryland, inda Halima Djimrao take zaune da maigidanta da ‘ya’yansu.

Na tambaye ta ko tunda suka rasa wuta cikin daren jumma’a sun sake ganin alamarta ya zuwa kamar awa uku da suka shige sai ta ce...

Bayanin Halima

A Kan Ruwa da Iska Da Dauke Wutar Lantarki

XS
SM
MD
LG