Accessibility links

Wasu fiye da 3o sun ji rauni alokacin da dan harin kunar-bakin-wake ya tayar da bam a harabar wani coci a unguwar Yelwa dake bayan garin Bauchi

Jami'an Najeriya sun ce wani dan harin bam na kunar-bakin-wake ya tuka wata motar da aka cika da nakiya zuwa cikin harabar wata Majami'a a yankin arewacin kasar jiya lahadi, ya kashe mutane akalla 15 a hari na baya-bayan nan da ake kaiwa kan Kirista a yankin.

Jami'an ayyukan gaggawa sun ce wasu mutanen su 42 sun ji rauni a wannan harin bam da ya wakana a daidai lokacin da masu ibada suke fitowa daga Majami'ar dake unguwar Yelwa a bayangarin Bauchi, babban birnin Jihar Bauchi.

Shaidu sun ce wannan bam mai karfin gaske ya sa bangaren cocin ya rushe, ya fadio a kan masu ibada, ya kashe fararen hula har ma da jami'an tsaro, yayin da ya haddasa mummunan rauni ma wasu.

babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin, amma a can baya an san cewa kungiyar nan ta Boko Haram tana kai hare-hare a kan majami'u.

An dora ma kungiyar ta Boko Haram alhakin kisan daruruwan mutane, ciki har da wasu munanan hare-haren da aka kai kan wasu majami'u ranar Kirsimeti aka kashe mutane fiye da 30 a kusa da Abuja, babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG