Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane akalla 7 sun mutu a wasu harbe-harbe a birnin Mogadishu


Dakarun gwamnatin Somaliya kenan ke rangadi a kasuwar Bakara da ke birnin Mogadishu

Shaidun gani da ido sun bada labarin cewa harbe-harben da aka rika yi

Shaidun gani da ido sun bada labarin cewa harbe-harben da aka rika yi da igogi a Mogadishu, babban birnin kasar Somalia yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla bakwai.

Shaidun gani da idon sun bayyana haka ne Safaiyar yau Talata, kuma anyi harbe-harebn a da tsakar dare. Daga cikin wadanda suka halaka a dalilin harbe-harben harda wasu iyalai da ‘ya’yansu biyu.

Harkokin tsaro sun fara ingantuwa a birnin Mogadishu tun daga lokacin da hadin gwiwar sojin Somaliya da na kungiyar tarayyar Afirka suka sami nasarar korar mayakan al-shabab daga birnin Mogadishun.

Amma duk da haka ana ci gaba da samun harbe-harbe jifa-jifa, da suka hada harda makaman roka.

Gwamnatin rikon Somalia na samun goyon bayan rundunar sojin tarayyar Afirka kuma a watan Fabarairun da aya gabata ne suka sami nasarar korar mayakan al-Shabab daga birnin Mogadishu.

XS
SM
MD
LG