Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Biyar Sun Mutu a Bala'in Zaizayar Kasar Indonesia


Ministan harkokin cikin gida na Indonesia, Tjahtjo Kumolo (Foto: VOA/Nurhadi)

Akalla mutum biyar suka mutu kana wasu 15 suka bata, bayan bala'in zaizayar kasar da ta afkawa wani tsibiri a Indonesia.

Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu, bayan da aka samu zaizayar kasa a Indonesia.

Bayanai sun ce wasu mutane 15 sun bata a wani kauyen da ke kan Tsibirin Java.

Wani kakakin, hukumar da ke sa ido kan aukuwar wani bala’i, ya ce, lamarin ya faru ne a yau Alhamis a tsibirin da ke Gundumar Brebes a tsakiyar yankin Java, a daidai lokacin da manoma ke aiki a gonakinsu na shinkafa.

Zaizayara kasar ta auku ne a cewar mazauna yankin, bayan da aka kwashe kwanaki da dama ana tafka ruwan sama, wanda hakan ya sa kasar tsaunukan da ke zagaye da yankin ta yi laushi.

Tuni aka baza sojoji da ‘yan sanda domin neman wadanda bala’in ya rutsa da su, inda suke amfani da fatanyu da kuma hannayensu wajen tonon kasa, saboda laka ta hana a yi amfani da manyan na'urori.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG