Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Da Dama Sun Mutu, Da Yawa Kuma Sun Ji Ciwo A Fashewar Bom a Maiduguri


Jami'an tsaro da mutanen gari na kokarin dauke gawarwaki da wadanda suka ji ciwo

Shaidu sun ce wasu matasa hudu daga Dambuwa ne suka dasa bom din a unguwar post office

Duk da cewa har yanzu ba a kididdige yawan wadanda harin bom din na unguwar post office ya rutsa da su ba, an tabbatar da cewa an yi mace-mace, kuma da yawa sun jikkata. Wakilin Sashen Hausa a Borno Haruna Dauda Biu ya koma wurin da bom din ya tashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Wani wanda ya bukaci a sakaya sunan sa ya shaidawa wakilin na Sashen Hausa cewa sun kama matashi daya daga cikin wadanda suka kai harin, kuma sun mika shi ga jami'an tsaro da ya fara magana ya na bayar da bayani a kan dasa bom din, kuma ya ce su hudu ne, ukun sun gudu.

Kakakin rundunar sojan shiyya ta bakwai kanal Muhammed Dole ya tabbatar da afkuwar lamarin sannan kuma ya yiwa Haruna Dauda Biu karin bayani.
XS
SM
MD
LG