Accessibility links

Mutane Da Dama Sun Rasu A Hadarin Jirgin Sama A Lagos

  • Grace Alheri Abdu

Hadarin wani jirgin sama a Najeriya.

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, wani karamin jirgin sama ya yi hatsari a tashar jirgin sama ta Murtala Mohammed dake birnin Ikko.

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, wani karamin jirgin sama ya yi hatsari a tashar jirgin sama ta Murtala Mohammed dake birnin Ikko.

Janar Manajan cibiyar agajin gaggawa ta jihar Lagos Dr. Femi Oke-Osayintolu, wanda ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Najeriya afkuwar hadarin ya ce fasinjoji 11 suka rasu yayinda aka dauki tara zuwa asibiti.

Akwai sabanin rahotanni kan wadanda suka mutu. Jirgin mallakar kamfanin Associated Airlines ne da aka ce ya dauki mutane 20 da suka hada da iyalan tsohon gwamnan jihar Ondo Olusegun Agagu da gawar mamacin a kan hanyarsu zuwa Akure inda za a yi jana’izarshi.

Bayanai na nuni da cewa, jirgin ya sami matsalar inji ne lokacin yana tashi.
XS
SM
MD
LG