Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pompeo Ya Dawo Gida Daga Asia


Mike Pompeo da shugaban Indonesia Joko Widodo
Mike Pompeo da shugaban Indonesia Joko Widodo

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya kammala rangadi da yake a kudu maso gabashin Asia.

Kafin ya bar yankin da safiyar yau Lahadi, ya gana da shugaban Indonesia Joko Widodo, inda ya fada masa cewa Amurka tana mutunta alakar tsakaninta da Indonesia, daya daga cikin kasashen duniya dake bin tafarki demokaradiya.

A jiya Asabar, babban jamai’in diflomasiyar Amurkan ya gana da takwaran aikinsa na Indonesia Rentro Marsudi. Sakataren da ministan harkokin wajen Indonesia sun tattauna a kan batutuwar ci gaba da bunkasa hadin gwiwa domin tinkarar matsalolin tsaron yankin, ciki har da batun Korea ta Arewa da kuma yaki da ta’addanci, da ma wasu batutuwar harkokin kasashen waje da na fahimtar juna.

Pompeo ya isa birnin Jakarta ne daga Singapore, inda aka yita samun bayanai masu cin karo da juna a kan alakar Amurka da Korea ta Arewa, duk kuwa da ci gaba da tattaunawar da ake yi a kan batun wargaza shirin makaman nukiliyar Korea ta Arewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG