Accessibility links

Mutane goma sha biyu suka rasa rayukansu a hare hren da aka kai a Gombe cikin daren jiya


Wani bangaren ofishin ‘yan sanda da aka kaiwa hari a Gombe.

Hukumar agaji ta Red Cross a jihar Gombe ta bayyana cewa mutane 12 suka rasa rayukansu yayinda wadansu biyar kuma suka ji raunuka a harin da aka kai jiya da dare

Saurari:

Hukumar agaji ta Red Cross a jihar Gombe ta bayyana cewa mutane 12 suka rasa rayukansu yayinda wadansu biyar kuma suka ji raunuka sanadiyar fashe fashen boma bomai da kuma harbin bindigogi da aka kaddamar a babban birnin jihar.

A cikin hirarshi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, sakataren kungiyar agaji ta Red Cross na jihar Gombe Abubakar Yakubu ya bayyana cewa, kungiyar agajin ta taimaka wajen ganon gawawwakin da kuma daukar wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Bisa ga cewarshi, an kona dukan ababan hawan dake harabar babban ofishin ‘yan sanda dake tsakiyar birnin da ake kira Divisional Police Station yayinda boma boman da aka dana suka lalata gine ginen ofishin. Abubakar Yakubu ya shawarci al’umma su kiyaye dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kafa domin kare lafiyarsu, yayinda jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG