Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Goma Sun Rasa Rayukansu a Kunar Bakin Waken Garin Gamboru-Ngala


Gawarwakin wasu daga cikin mutanen da suka mutu a harin kunar-bakin-wake da aka kai wani Masallaci a garin Gamboru-Ngala, laraba 3 Janairu 2018

Gamboru Ngala, garin dake kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru ya samu kunar bakin waken da yahallaka mutane goma cikin masallaci a karon farko tun lokacin da jama'a suka koma garin bayana an kakkabe 'yan Boko Haram

Da safiyar yau Laraba wani bam ya tashi cikin wani masallacin dake garin Gamboru Ngala, garin dake kan iyaka da kasar Kamaru.

Tashin bam din ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara dake salla cikin masallacin tare da dan kunar bakin waken da ya sa adadin wadanda suka mutun ya kai goma.

Lamarin ya auku ne a daidai lokacin da ake sallar asuba inda dan kunar bakin waken ya kutsa cikin masallacin dake anguwar Abuja. Na take ya tada bam dake cikinsa ya hallaka kansa da mutane taran dake salla a masallacin. Babu wanda ya tsira.

Wannan harin shi ne na farko da aka samu tun lokacin da mutane suka koma garin bayan an kwatoshi daga hannun 'yan Boko Haram da suka mamayeshi na wani dan lokaci.

Wani mazaunin garin ya yiwa Muryar Amurka karin bayani akan aukuwar lamarin. Ya tabbatar cewa harin cikin masallaci ya auku. Wanda ya kai harin shekarunsa zasu kai talatin da biyar. A cewarsa babu wanda ya jikata domin mutane taran dake salla a masallacin su ne suka mutu tare da dan kunar bakin waken. Harin ya rutsa da masallacin da mutane taran dake salla a ciki.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG