ADAMAWA, NIGERIA - Jauro Mamudu da ke zama jauron Mayine Worolamido ya tabbatar da cewa ba karamar wahala su ke sha ba saboda rashin malaman jinyan a yankin.
Shi ma Alhaji Abubakar, wani dattijo a yankin, kuma shugaban kungiyar da ke asibitin, ya tabbatar da rashin malaman jinya a asibitan.
Abubakar Aliyu Liman stohon kansila mai wakiltar Mayo a majalisar karamar hukumar Fufore kuma dan garin Worolamidon na yankin da yake fama da matsalar rashin ma’aikatar jinya ya ce lallai lamarin ya janyo musu asarar rayuka da dama agarin nasu.
Mun nemi sakataren hukumar kiwon lafiya na karamar hukumar Fufore don jin karin bayani dan gane da lamarin, ya ce zai yi bincike akai amma daga bisani kuwa mun sake buga masa waya bai dauka ba mun kuma aika masa da sako, yanzu har kwana uku shiru ka ke ji.
Saurari rahoton daga Lado Salisu Muhammad Garba: