Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Shida Suka Mutu A Harin Da Aka Kai Garin Potiskum


Mutane suna tsaye kusa da wani wurin da kungiyar Boko Haram ta kai hari

Yau lahadi da tsakar rana ne wani dan kunar-bakin-wake cikin wata mota kirar Honda Civic ya kashe kansa da wasu mutanen da dama a wata tashar da ake lodin fasinja a gefen hanya kusa da gidan man da ake kira IBAL a kan hanyar Jos a garin Potiskum, Jihar Yobe.

Da yake bayyana ma Dandalin VOA abinda ya faru, wani ganau yace dan kunar-bakin-waken yayi kokarin shiga inda jama'a suke da yawa, amma bai samu sa'a ba sai motar ta tashi da shi.

Nan take ya kashe wata yarinya mai tallen goro da ta yi zaton zai tsaya sayen goro ne a lokacin da ya nemi yin ribas da motarsa.

Mutane akalla biyar suka mutu a bayan shi dan ta'addar da ya kai wannan harin.

Garin na Potiskum yana fuskantar hare-haren bam na 'yan ta'adda sosai a cikin 'yan watannin nan, ciki har da wanda aka kai kan makarantar sakandare, da wanda aka kai kan ;yan mazhabin Shi'a, da kuma wanda aka kai kwanakin nan a kan kasuwar wayar hannu.

Saurari cikakken bayanin abubuwan da suka wakana a lokacin harin na yau lahadi...

Cikakken Bayanin Tashin Bam Yau Lahadi A Potiskum - 6'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG