Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Sun Taru Makil Wajen Jana'izar Muhammad Ali


Jana'izar Muhammad Ali
Jana'izar Muhammad Ali

Dubban mutane ne bakar fata da farare, musulmi da yahudawa da kiristoci, matsa da tsoffi ne suka cika makil a babban zauren taro a birnin Louisville a jihar Kentucky jiya Alhamis, domin jana'izar dan damben nan Muhammed Ali.

Zakarar damben, wanda dubban miliyoyin jama'a suka sani a fadin duniya, ya rasu ne makon jiya yana da shekaru 74 bayan shekaru yana fama da cutar makyerketa ko Perkinsons da turanci.

Anyi addu'o'in ne a wurin da Muhammed Ali yayi dambensa na farko a garin da aka haifeshi a shekarar 1960, jim kadan bayan da ya sami lambar zinari a gasar Olympic da aka yi a Roma.

Musulmai da masu karrama shi duk suka ce Muhammed Ali shine "alamar muslunci" mutumin da yake karfafa zaman lafiya da mutunta mabiya wasu addinan.

Yau Jumma'a za'a yi masa wasu addu'o'i na musamman a zaman hadin guiwa na mabiya addinai daban daban a birnin na Lousiville dake jihar ta Kentucky.

XS
SM
MD
LG