Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Tara Sun Rasa Rayukansu a Somaliya


Wasu dakarun Afirka masu wanzar da zaman lafiya a Somaliya
Wasu dakarun Afirka masu wanzar da zaman lafiya a Somaliya

Biyo bayan harin da kungiyar al-Shabab ta kai kan sansanin sojojin Afirka masu wanzar da zaman lafiya a kasar mutane tara suka rasu

A Somaliya rundunar dakarun hadin gwiwar kasashen Afirka wato AU ta bayyana cewa mutane 9 ne suka rasa rayukansu biyo bayan wani hari da mayakan al-Shabab suka kaiwa sansaninsu a kusa da babbar tashar jirgin sama na kasa da kasa a Mogadishu.

Rundunar dake ayyukan wanzar da zaman lafiya a Somaliya ko AMISOM a takaice, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa mayakan al-Shabab sanye da kayan sojojin Somaliya suka haura zuwa harabar sansanin da rana jiya Alhamis.

Sanarwar ta kara da cewa mayaka biyar, tare da sojojin AU guda 3 da wani farin hula daya ne suka rasa rayukansu a harin, sannan an cafke wasu mayakan al Shaban guda uku.

Rundunar AMISOM ta bayyana cewa yanzu haka tana rike da ikon sansanin, kuma ayyuka sun cigaba kamar yadda suka saba.

A lokacin da take daukar alhakin harin, kungiyar al Shaban tace manufarta shine kaiwa wani taron shakatawa hari a sansanin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa kungiyar tayi ikirarin kashe mutane 14.

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG